Essien ya tsawaita kwantiraginsa da Chelsea

Michael Essien

Dan wasan tsakiya na kulob din Chelsea Micheal Essien ya sake sanya hannu a wata kwantiragin da za ta tsawaita zamansa a kulob din da karin shekara biyu.

Hakan dai na nufin dan wasan zai ci gaba da zama a Stamford Bridge har zuwa shakarar 2015.

Essien mai shekaru 27, wanda ya koma kulob din Chelsea daga Lyon a shekarar 2005, bai buga wa kulob din wasa ba tun watan Disambar da ya gabata bayan ya samu rauni a agararsa.

Ba kuma zai taka leda a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Afrika ta Kudu ba saboda raunin da ya samu a gwuwar kafa a watan Janairun da ya gabata.

Kulob din Chelsea dai ya sayi dan wasan ne daga Lyon a kan kudi fam din Ingila miliyan ashirin da hudu, ya kuma ci wa kulob din kwallaye 22 a wasanni 185 da ya buga.