Ferdinand ba zai taka leda a Afriak ta Kudu ba

Rio Ferdinand
Image caption Rio Ferdinand ya dade yana fama da rauni

A yanzu dai ta tabbata cewa kyaftin din Ingila Rio Ferdinand ba zai taka leda a gasar cin kofin duniyar da za a fara a Afrika ta Kudu ba, bayanda ya samu rauni.

Dan wasan mai shekaru 31, ya samu rauni ne a gwuiwarsa bayan da yayi karo da Emile Heskey a ranar Juma'a, sannan aka garzaya da shi asibiti, amma daga bisani ya bar asibitin, yana dogara sanda.

Tunda farko kociyan kasar ya bayyana fata nagari kan dan wasan inda yace: "Muna fatan babu wata matsala sosai, amma mun gayyato Michael Dawson domin jiran ko ta kwana," a cewar kociyan Ingila Fabio Capello.

Amma bayan an sake duba shi, sai ta tabbata cewa ba zai warke akan lokaci ba, ballantana ya iya taka leda a gasar ta bana.

Masana na ganin wannan ba karamin kalubale bane ga kasar ta Ingila, a kokarin da take yi na taka rawar gani a gasar.

Shi ma mai tsaron gida David James bai yi atisayi ba saboda yana fama da wani dan rauni, amma dan tsakiya Gareth Barry yayi atisayi.

"Mummunan labarin shi ne na raunin da Rio ya samu, ya samu rauni a gwuiwar sa," inji Capello

Dama dai Ferdinand ya sha fama da rauni a kakar wasanni ta bana, inda ya buga wasanni 21 kacal a klub din sa na Manchester United.