Libya ta daina buga wasa da Algeriya da Masar

'Yan sandan Sudan
Image caption 'Yan sandan Sudan lokacin da suke kokarin shawo kan rikicin Masar da Algeriya

Mahukunta a Libya sun dakatar da kungiyoyin wasa na kasar daga karawa da takwarorin su na Masar da Algeriya.

Suma kungiyoyin kwallon kafa na kasar wajibi ne su nemi izini daga hukuma kafin su kara da sauran takwarorin su na kasashen Larabawa. Za su nemi izinin ne domin samun "hadin kai ta fuskar wasanni", amma ba a bada dalili ba kan haramcin da aka sanya kan Masar da Algeriya.

Sai dai wakiliyar BBC a Libya Rana Jawad, tace wasu na alakanta wannan matakin da tashin hankalin da ya biyo bayan karawar da aka yi tsakanin Masar da Algeriya bara.

Sabbin dokokin dai na kunshe ne a wata sanarwa da aka aikewa hukumomin da abin ya shafa a kasar, wacce kuma manema labarai suka samu. Wani jami'i a Hukumar Kwallon kafa ta Libya, ya shaidawa BBC cewa yana fatan za a sauya matakin a lokacin da Libya za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara ta 2013.