Nani ba zai taka leda ba a Afrika ta kudu

Nani
Image caption Nani ya taka rawar gani a wasanni cancantar taka leda a gasar cin kofin duniya

Dan wasan Portugal Nani ba zai samu damar taka leda ba a gasar cin kofin duniya da za a fara a kasar Afrika ta kudu ranar Juma'a, saboda raunin da ya samu a kafadarsa.

"Mun gwada shi kuma mun tantance cewar ba zai iya taka leda ba a gasar cin kofin duniya". Inji Sanarwar da tawagar kasar ta bayar.

Dan wasan dake takawa kungiyar Manchester United leda a Ingila ya samu raunin ne a lokaci da ya ke horo da tawagar kasar a birnin Lisbon a ranar Juma'ar da ta gabata. Dan wasan mai shekarun haihuwa 23 ya zura kwallaye uku ne a wasanni cancantar taka leda zuwa kasar Afrika ta kudu.

A yanzu haka dai dan wasan Benfica Ruben Amorim zai maye gurbinsa.