An gargadi Rooney da ya gyara halinsa

Rooney da alkalin wasa Selogilwe
Image caption Alkalin wasan Selogilwe ya gargadi Wayne Rooney da ya rage zuciya.

Alkalin wasan da jagoranci wasan sada zumuncin da Ingila ta buga da Platinum Stars, ya gargadi Wayne Rooney da ya rage zuciya lokacin wasa, ko kuma ya fuskanci kora a lokacin gasar cin kofin duniya.

An dai bawa Rooney katin gargadi a wasan da Ingila ta lallasa Platinum Stars da ci 3-0, bayanda alkalin wasa Jeff Selogilwe, yace Rooney ya gaya masa bakar magana.

Selogilwe yace: " Ya kamata ya rage zuciya, idan ba haka ba to zai fuskanci kora daga wurin alkalai a gasar da ake shirin farawa ranar Juma'a".

Rooney, dan shekaru 24, yayi nadama a karshen wasan, sannan ya nemi gafarar alaklin wasan har ma ya bashi kyautar rigarsa.

Kafin fara wasan dai sai da mataimakin kyaftin din Ingila Frank Lampard, ya gargadi takwarorin na sa da su kaucewa tashin hankali idan har suna son samun nasara a gasar.

Rooney ya taimakawa Joe Cole ya zira kwallo daya sannan ya ci daya da kansa, bayan Jermain Defoe ya zira kwallon farko. Sai dai Rooney ya nemi fada tsakanin sa da Kagiso Senamela na Platinum Stars, bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Mai yiwa BBC sharhi kan al'amuran kwallon kafa Phil McNulty yace: " Idan har Rooney zai tada jijiyar wuya a wannan karamin wasa, to ya zai yi idan aka fara gasar cin kofin duniya gadan-gadan".