Ballack da Joe Cole za su bar Chelsea

Joe Cole
Image caption Joe Cole ya dade yana taka leda a Chelsea

Rahotanni na nuna cewa Michael Ballack da Joe Cole na shirin barin kungiyar Chelsea, a lokacin musayar 'yan wasa na kakar wasanni ta bana.

Cole, dan shekaru 28, zai bar klob din a farkon watan Yuli, bayan da rahotanni suka nuna cewa kungiyar ta ce ba za ta sabunta kwantiragin sa ba.

Ya dai zo klub din ne daga kungiyar West Ham a shekara ta 2003, kuma a yanzu yana Afrika ta Kudu domin takawa Ingila leda a gasar cin kofin duniya.

Shi ma Ballack na Jamus, mai shekaru 33, wanda yazo Chelsea a shekara ta 2006, ba za a sabunta kwantiragin sa ba.

A da dai shi ne zai jagoranci Jamus a gasar cin kofin duniya amma rauni ya hana shi.

A watan Juni ne kwantiraginsa za ta kare, kuma ya shaidawa wata kafar yada labarai ta Jamus cewa ya fi so ya ci gaba da taka leda a Chelsea.