Takaittaccen tarihin Brazil

Tawagar Brazil
Image caption Tawagar Brazil na murnan lashe gasar cin kofin duniya a gasar da aka shirya a Koriya da Japan a 2002

Brazil dai ta lashe gasar kofin duniya, har sau biyu a baya.

A wasan cancantar taka leda zuwa kasar Afrika ta kudu brazil din ta lashe wasanni tara ne a yayinda ta buga kunnen doki a wasanni bakwai sannan kuma an doke ta a wasanni biyu.

Wannan al'amari dai ya janyo wa tawagar kasar suka daga masoya kwallon kafa a kasar, saboda matsalolin da ta fuskanta.

Tawagar kasar karkashi jagorancin kocinta Carlos Dunga, na fuskantar matsin lamba daga masoya kwallon kafa na kasar domin su lashe gasar, ganin irin tarihi da kasar ta kafa a baya.

Wanan dai shine karo na goma sha shida da kasar ke halartar gasar a jere, kuma itace kasa daya tilo data halarci duk gasar kofin duniya da aka shirya.

A wasanni casa'in da biyu da kasar ta buga a gasar gabaki daya, ta lashe wasanni sittin da hudu ne, a yayinda ta buga canjaras a wasanni goma sha hudu an kuma doke ta a wasanni goma sha hudu.

Tsakanin ranar goma sha biyar ga watan yunin shekarar 2008 da ranar goma sha daya ga watan Oktoban shekarar dubu biyu da tara, babu wata kasa da ta doke Brazil a duniya.

Brazil dai za ta fafatane a rukunin Gaa tare da kasar Portugal da Koriya ta arewa da kuma Ivory Coast.