Rafael Benitez ya koma Inter Milan

Rafael Benitez
Image caption Rafael Benitez ya taka rawar gani a Livepool

Inter Milan ta bada sanarwar cewa tsohon kociyan Liverpool Rafael Benitez, ya amince ya zamo sabon kocin kungiyar.

"Mun cimma matsaya, mun kammala duk wani abu da ke da mahimmanci," shugaban Inter Massimo Moratti, yana shaidawa kamfanin dillancin labarai na Ansa. Moratti yace a ranar Talata Inter za ta bada cikakken bayani kan shirye-shiryen gabadar da Benitez a matsayin sabon kocin ta.

Benitez, dan shekaru 50, ya bar Liverpool a makon da ya gabata bayan shafe shekaru shida, kuma zai maye gurbin Jose Mourinho ne a Inter Milan. Moratti ya kara da cewa basu tattauna kai tsaye da Benitez ba, amma zai isa birnin Milan a makonnan domin kammala yarjejeniyar da za ta ba shi damar komawa klob din.

"Abinda kawai ya rage a yanzu shi ne na sanya hannu kan kwantiragi," a cewar shugaban Inter Masimo Moratti.