Takaitaccen tarihin kwallon Najeriya

Najeriya nada kwararrun 'yan wasa
Image caption Najeriya nada kwararrun 'yan wasa

Ko da yake dai Najeriya bata shiga cikin gasar da akayi a Jamus ba a shekara ta 2006.

Amma dai, masu sharhi na yi mata kallon kasar da Allah ya albarkata da 'yan wasa wadanda idan har suka samu kwararren koci, tabbas zasu iya girgiza duniya.

Koda yake dai Najeriya bata taba wuce zagaye na biyu ba a gasar cin kofin duniya.

Amma dai a wannan karon karkashin jagoranci koci Lars Lagerback da kuma 'yan wasa kamar su Mikel Obi da Martins Obafemi da kanu Nwankwo, kasar za ta yi kokarin kaiwa a kalla zagayen gabda na kusa da karshe.

Babban kalubalen dake gaba Super Eagles shine tsallakewa daga cikin rukunin da take wanda ya kunshi Argentina da Girka da kuma Koriya ta Kudu.

Kuma za su kara ne a rukuni guda da kasashen Argentina da Girka da kuma Koriya ta Kudu.