Viera na son ci gaba da zama a Man City

Patrick Vieira da Roberto Mancini
Image caption Patrick Vieira da Kocin Manchester City Roberto Mancini, a lokacin da kungiyar ke gabatar da shi

Patrick Vieira ya ce ya nada burin ci gaba da zama a kungiyar Manchester City a kakkar wasa mai zuwa.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 33 ya sa hannu ne a kwantaragin wata shida domin takawa kungiyar City leda a kakar wasan bara.

"Ina son ci gaba da zama a Manchester City kuma kungiyar na so in zauna". Inji Viera a hirarsa da BBC.

"Ina da kwarin gwiwa cewar zan buga wasa a kungiyar, a kakar wasa mai zuwa. Kungiyar ta sayo ni ne domin in taimaka mata, kuma ina ganin ina da kwarewar da zai taimaka mata".

Vieira dai ya koma kungiyar City ne a ranar 8 ga watan Janairun wannan shekara, kuma shine ya zama dan wasa na farko da kocin kungiyar Roberto Mancini ya saya bayan ya kama aiki.