Vieira zai kara shekara daya a Manchester City

Patrick Vieira da Roberto Mancini
Image caption Patrick Vieira da Roberto Mancini

Kungiyar Manchester City ta Ingila ta ce Patrick Vieira zai ci gaba da zama a kungiyar na tsawon shekara guuda bayan kwantaraginsa na wata guda ya cika.

Dan wasan mai shekarun haihuwa talatin da uku na kowa kungiyar ne daga Inter Milan a watan Junairun da ta gabata.

"Ina son ci gaba da zama a Manchester City kuma kungiyar na so in zauna". Inji Viera a hirarsa da BBC.

"Kungiyar ta sayo ni ne domin in taimaka mata, kuma ina ganin ina da kwarewar da zai taimaka mata".

Vieira dai ya koma kungiyar City ne a ranar 8 ga watan Janairun wannan shekara, kuma shine ya zama dan wasa na farko da kocin kungiyar Roberto Mancini ya saya bayan ya kama aiki.