An sabunta: 11 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 09:35 GMT

Karawa tsakanin Faransa da Uruguay

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Tawagar 'yan kwallon Uruguay

Tawagar 'yan kwallon Uruguay

Kasar Faransa za ta kara da Uruguay awasa na biyu da za a buga a rukunin A a garin Cape Town.

Faransa wacce ta lashe gasar a shekara ta 1998, bata taka rawar gani a kan hanyarta ta zuwa Afrika ta Kudu ba.

Kuma ana saran kyaftin din kasar Thierry Henry ba za a fara wasan da shi ba, amma William Gallas ya warke daga raunin da ya samu, kuma ana saran zai taka leda.

Itama dai Uruguay ba kanwar lasa bace ganin irin 'yan wasan da take da su, kamar su Diego Forland na Atlethico Madrid.

Wannan rukuni na A, ya kunshi kasashen Afrika ta Kudu da Mexico.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.