An sabunta: 11 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 09:32 GMT

An fara gasar cin kofin duniya

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Mai masaukin baki Afrika ta Kudu ta kara da kasar Mexico, a wasan farko na gasar cin kofin duniya da ake karawa a kasar Afrika ta Kudu. An tashi 1-1.

Sai dai tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela bai halar ci gasar cin kofin duniyar da aka fara a birnin Johannesburg ba.

Hakan ya biyo bayan mutuwar tattaba kunnen sa Zenani wacce tayi hadarin mota akan hanyarta ta komawa gida daga wajen bikin bude gasar.

Ofishin mista Mandela ya fidda wata sanarwa inda yace tsohon shugaban ba zai halacci gasar ba, saboda mutuwar tattaba kunnen ta sa.

Ada dai ana saran Mista Mandela zai halarci bikin bude gasar na dan wani lokaci.

Wannan ne karo na 19 da za ayi gasar, kuma karo na farko da wata kasar Afrika ta dauki bakunci.

A filin wasa na birnin Soccer City, wanda ke daukar 'yan kallo 94,000, aka gudanar da wasan farko da misalin karfe hudu.

Shahararren mawakin nan na Amurka R Kelly na daya daga cikin mawaka 1,581 wadanda suka yi wasa a wurin bikin bude gasar.

Ana saran jama'a daga kasashe 215 ne za su kalli gasar, wadanda yawan su ya kai daruruwan miliyoyi.

"Ta riga ta yi gaba"

Shugaban kasar Jacob Zuma da Atbishop Desmond Tutu ne ya jagoranci bikin tare da jami'an hukumar kwallon kafa ta FIFA.

"Afrika ta Kudu ta riga tayi gaba, kuma ba za ta koma baya ba," a cewar Mista Zuma, wanda ya yabawa rawar da tsohon shugaban kasar Nelson Mendela ya taka wajen kawo gasar kasar.

Makada algaitar Vuvuzela

Algaitar Vuvuzela tana karawa 'yan wasan Afrika ta Kudu kaimi

Ana saran gasar za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Daga cikin shahararrun 'yan wasan duniya da za su halarci gasar sun hada da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Wayne Rooney.

Sai dai wasu dama za a yi babu su, kamar su Rio Ferdinand da David Beckham da Michael Ballack da Michael Essien na Ghana.

Ingila wacce na daya daga cikin kasashen da ake saran za su taka rawar gani, za su buga wasan su na farko a ranar Asabar.

Masu rike da kanbun Italiya za su fara nasu wasan a ranar Litinin da Paraguay, Brazil za ta kara da Koriya ta Arewa ranar Talata, yayinda Najeriya za ta kara da Argentina ranar Asabar.

Afrika ta Kudu bata taba wuce zagayen farko ba, yayinda akewa New Zealan da Koriya ta Arewa kallon kurar baya.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.