An sabunta: 19 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 13:36 GMT

Holland 1Japan 0

A karawar da aka yi tsakanin kasashen Holland da Japan, an tashi ne Holland tana da ci daya, Japan na nema.

Japan dai ba ta taba wuce wa zagayen farko a gasar cin kofin duniya a wajen kasarsu ba.

Sai dai nasarar da suka samu a kan kasar Kamaru a wasan da suka kara ranar Litinin din da ta gabata ta dada musu karfin gwuiwar yiwuwar cimma hakan.

Kafin karawr ta yau dai, Karawa daya tilo da kasashen biyu suka taba yi tsakaninsu ita ce wadda aka yi a watan Satumbar shekarar da ta gabata, inda Holland ta lallasa Japan da ci uku da nema.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.