An sabunta: 13 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:57 GMT

Gasar kofin duniya:Ghana ta ci Serbia daya da nema

Ghana ta yi nasara akan kasar Serbia da ci daya da nema a wasan da suka yi a Pretoria.

Ghana ta ci kwallon ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Wannan ne dai karo na biyu da kasashen Serbia da Ghana ke haduwa da juna a wasan kwallon kafa.

Haduwarsu ta farko dai an yi ta ne a shekarar 1997, inda tsohuwar kasar Yugoslaviya ta lallasa Ghana da ci uku da nema a gasar da cin kofin Korea.

Za kuma a kara a yau din tsakanin Jamus da Australia.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Jamus da Australia

Jamus da Australia sun taba karawa da juna sau biyu a baya.

Karawa ta farko a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a shekarar 1974, inda Jamus ta baiwa Australia kashi da ci uku ba ko daya.

Kasashen biyu sun sake yin karon batta a gasar cin kofin Confederation na shekarar 2005 da ta gudana a kasar Jamus, kuma masu masaukin baki wato Jamus, su ne suka sake samun nasara da ci 4-3.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.