An sabunta: 14 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 15:21 GMT

Karawa tsakanin Italiya da Paraguay

Italiya wacce za ta fara yunkurin kare kanbunta a gasar ta bana akarawar da za ta yi da Paraguay a rukunin F. Wannan wasa dai na da mahimmanci wajen tantance wanda zai jagoranci rukunin.

Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da Italiyan ke fara irin wannan gasa da alamun tambaya a kanta ba.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Masana na zargin cewa 'yan wasan na Italiya sun tsufa da yawa, ganin cewa tara daga cikin su sun taka halacci gasar da ta gabata a shekara ta 2006.

Amma kociyan kasar Marcelo Lippi yayi watsi da wannan zargi, yana mai cewa ashirye yaran sa suke.

Itama dai Paraguay ba kanwar lasa bace, ganin yadda ta zamo ta uku a gasar share fagen da aka gudanar a yankin kudancin Amurka.

Daga cikin 'yan wasan da ake saran za su nuna kwarewa a wasan sun hada da Salvador Cabanas na Borussia Dortmund, wanda ya zira kwallaye 19 a gasar Bundesliga.

A bangaren Italiya dai akwai tsohon gwarzon dan kwallon duniya Fabio Cannavaro da Gelluca Buffon wadanda dukan su suka fuskanci rashin nasara da kungiyar Juventus a kakar wasan da ta gabata.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.