Italiya 1-1 Paraguay

Karawa tsakanin Italiya da Paraguay
Image caption Karawa tsakanin Italiya da Paraguay

An ta shi daya da daya tsakanin mai rike da kanbun kwallon duniya Italiya da kuma Paraguay a rukunin F.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ne dai Paraguay ta jefa kwallon farko bayan da samu firikik.

Amma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sai Italiya ta farke kwallonta ta hannun Di Rossi.

Abinda yasa akai ta yin turmun danya, yayinda Italiya tayi ta kai farmaki, amma ba tare da nasarar kara kwallo ba.

Wannan wata dama ce ga kasashen New Zealand da Slavakia wadanda za su kara gobe a daya wasan na rukunin F.