Brazil ta doke Koriya ta Arewa da ci biyu da daya

Brazil ta doke Koriya ta Arewa
Image caption 'yan wasan Koriya sun taka rawar gani a wasan

Brazil ta doke Koriya ta Arewa da ci biyu da daya a wasan da kasashen biyu suka buga a rukunin G, a gasar cin kofin duniya dake gudana a kasar Afrika ta kudu.

Kafin a tafi hutun rabin lokaci dai, an tashi wasan ne babu ci.

Maicon ne da Elano su ka zurawa Brazil kwallayen bayan an dawo hutun rabin lokaci sanan kuma dan wasan Koriya Jui Yun Nam ya fanshe kwallo guda ana sauran minti uku kafin a tashi wasan.

Ganin irin zaratan 'yan wasan da Brazil ke da shi da kuma tarihin da ta kafa a baya, masana sunyi harsashen cewar, kasar za ta lallasa Koriya ta Arewa a wasan da kwallaye da dama.

Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyar, yayinda Koriya ta arewa ce ta tamanin da biyar a duniya cikin jerin kasashen dake tamoula a duniya.

Yanzu dai Brazil ce ke jagoranci a rukunin G , da maki uku bayan Portugal da Ivory Coast sun tashi babu ci a wasan da suka buga.