An sabunta: 15 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:05 GMT

Karawa tsakanin Ivory Cost da Portugal

Tarihi ya nuna cewa Wannan itace karawa ta farko tsakanin kasashen biyu agasar cin kofin duniya. Za dai su karane a wasan farko na rukunin G, wanda ake ma kallon mai sarkakiya.

Ivory Cost na neman taka rawar gani a gasar ganin irin fatan da ake da shi akanta, ganin irin kwararrun 'yan wasan da take da su.

Sai dai ba karamin kalubale bane a gaban su ganin cewa za su kara ne da Portugal karkashin jagorancin dan wasa mafi tsada a duniya Christiano Ronaldo.

Abinda yasa ake ganin wasan zai kayatar matuka gaya.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Sauran 'yan wasan da ake saran za su nuna kwarewa a wasan sun hada da kyaftin din Ivory Cost Didier Drogba, wanda hukumar FIFA ta amince ya buga wasan a yau, da Solomon Kalou na Chelsea da kuma Yaya Toure na Barcelona.

A watan Maris din bana ne aka nada Sven-Goran Eriksson a matsayin kociyan Ivory Cost, abinda yasa wasu keganin akwai kalubale a gaban sa sosai.

"Idan muka lashe wannan wasa to hakika za mu samu kwarin guiwa, zan so nayi kokari sosai, domin kasancewa dan wasan da yafi kowanne," in ji Ronaldo.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.