David Moyes ya kare Robert Green

Mai tsaron gida na Ingila
Image caption Wannan kuskure ya janyowa Ingila koma baya a wasan ta da Amurka

Kociyan Everton David Moye ya kare mai tsaron gida na Ingila Robert Green, bayan da ya yi kuskure a wasan da kasar ta buga da Amurka.

Kuskuren da Robert Green yayi ne dai ya janyo Amurka ta farke kwallon da Ingila ta zira mata, inda aka tashi wasa daya da daya.

A wata hira da BBC, Mista Moyes ya ce kowanne dan wasa yana iya kuskure, don haka wannan ba sabon abu bane.

Yace babu laifi idan kociyan Ingila Fabio Capello ya sake yin amfani da dan wasan a karawar da za su yi da Aljeriya.

" Ba na zaton Aljeriya za ta samu damar kaiwa Ingila hare-hare, don haka ba matsala idan aka sake amfani da Robert Green."

Ya kara da cewa yana da wuya kociya ya ajiye kowanne dan wasa, amma yanzu hankali ya koma kan Fabio Capello domin ganin matakin da zai dauka.

Tuni dai 'yan wasa da dama suka koka game da samfurin kwallon da ake amfani da ita, suna masu cewa ta yi santsi da yawa.