An sabunta: 16 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 10:50 GMT

Karawa tsakanin Honduras da Chile

karawa tsakanin Honduras da Chile

'yan kallo sun hallara domin kallon wasan Honduras da Chile

Honduras da Chile za su fafatawa a rukunin karshe na H, a ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

Sai dai wasu na ganin cewa sauran kasashen ukun da ke wannan rukunin za su bige da neman raka Spaniya zagaye na gaba ne, ganin yadda Spaniyan ke taka rawa a 'yan shekarunnan.

Abinda yasa kuma wannan wasan keda mutukar mahimmanci ga kasashen biyu.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

A wajen fili dai ana yiwa Chile kallon kan gaba, ganin tana dauke da dan wasan da yafi kowanne zira kwallaye a gasar share fage ta yankin kudancin Amurka.

Sai dai akwai shakku kan lafiyar dan wasan na Real Zaragoza Humberto Suazo, wanda na daya daga cikin wadanda ake saran za su taka rawar gani.

Shi ma David Suazo na Honduras na fama da makamanciyar wannan matsala, wata matsala ga kasar kuma itace ta ficewar Julio Cesar daga gasar baki daya saboda raunin da ya samu.

"Chile na da kwarewa sosai, suna rike kwallo a tsakiya, sannan ba za su baku damar walawa ba, don haka muna bukatar rike kwallo sosai, tare da hanasu motsawa,"in ji Thomas na Honduras.

Wannan rukuni dai ya kunshi kasashen Spaniya da kuma Switzerland, wadanda za su kara idan an jima da yamma.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.