Andy Murray ba zai buga Davis Cup ba

Andy Murray
Image caption Andy Murray ya dan kwanta dama a 'yan kwanakin nan

Andy Murray yan fice daga tawagar Burtaniya da za ta fafata da Turkiyya a wasan kifa daya kwale na gasar Davis Cup a watan gobe.

Bayan da tuni Alex Bogdanovic ya fice daga tawagar, a yanzu Burtaniya za ta buga wasan ne ba tare da manyan 'yan wasan Tennis biyu na kasar ba.

An dai tsara wasan ne a ranakun 9-da kuma 11 ga watan Julin bana.

Idan har Burtaniya ta sha kashi a karawar ta birnin Santambul, to za ta fada matakin karshe na gasar wato Euro-Africa Division Three.

Amma Murray, wanda ke kokarin shiryawa gasar Wimbledon, na ganin ya kamata a baiwa sabbin jini dama.

Dan wasan, wanda shi ne na daya a Burtaniya, ya shaidawa kyaftin Smith cewa: "Ina da dalilai da dama, ina ganin ya kamata mu fara baiwa yara dama sosai ko ma samu nasara".