Spaniya 0-1 Switzerland

Karawa tsakanin Spaniya da Switzerland
Image caption Karawa tsakanin Spaniya da Switzerland

Daya daga cikin kasashen da ake saran za su lashe gasar cin kofin duniya Spaniya, ta sha kashi a hannun switzerland da ci daya da nema.

Wannan dai shi wasa na farko da za a iya cewa sakamakon sa ya bada mamaki.

A minti na 52 ne Fernandes ya zira kwallon bayan wata arangama da akayi tsakanin mai tsaron gidan Spaniya da kuma 'yan bayan sa.

'yan wasan Spaniyar dai sun iya yinsu domin ganin sun rama kwallon amma hakar su bata cimma ruwa ba.

Spaniya ce dai ke rike kofin zakarun kwallon kafa na nahiyar Turai, kuma wannan sakamakon zai zowa 'yan kasar dama sauran masu sha'awar kwallo mamaki.

Hakan dai na nufin Spaniya ce ta karshe a rukunin na H, inda Chile da Switzerland ke kan gaba da maki uku-uku.