Farnsa 0-2 Mexico

Karawa tsakanin Faransa da Mexico
Image caption Yanzu dai tana-kasa-tana-dabo kan makomar Faransa a gasar

Mexico ta doke Faransa da ci biyu da nema a ci gaba da gasar cin kofin duniya da a keyi a Afrika ta Kudu.

Wannan ne dai karo na farko a tarihi da Mexico da taba lashe Faransa a wasan kasa da kasa.

Dan wasan Mexico Harnendez ne ya fara zira kwallo a minti na 64, bayan da yayi taho mugama da mai tsaron gidan Faransa.

Yayinda kyaftin Blanco ya zira kwallo ta biyu a minti na 79, bayan da a ka samu bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kuma hakan na nufin Uruguay da Mexico ne kan gaba a rukunin na A da maki hur hudu.

Yayinda a daya bangaren Faransa da Afrika ta Kudu mai masaukin baki suke da maki daya daya.

Idan har Faransa bata kai zagaye na biyu ba, to za ta maimaita gasar shekara ta 2002, inda aka fitar da ita a zagayen farko.