An sabunta: 17 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:58 GMT

Karawa tsakanin Faransa da Mexico

Karawa tsakanin Faransa da Mexico

Faransa ta tashi babu ci a wasan ta na farko da Uruguay

Bayan rashin katabus din da suka yi a karawar su ta farko da Uruguay, har yanzu kociyan Faransa Raymond Domenech, ba shi da tabbas a kan dabarun da zai fito da su.

Duk da cewa Faransa bata yi nasara awasanni biyar data buga a baya ba, Mexico bata taba yin nasara akan ta ba.

Ana ta bangaren Mexico za ta so ganin ta kara kokari kan daya da dayan data buga da Afrika ta Kudu a wasan farko.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Ana saran Mexico za ta yi amfani da dan gaban Arsenal Vela, wanda zai fafata da takwarorin sa na Arsenal din, kamar su William Gallas da Bacary Sagna.

Daga cikin 'yan wasan da ake saran za su taka rawar gani a wasan sun hada da Vela da Diaby, wadanda dukkan su suka taka rawar gani a wasan farko.

Tarihi ya nuna cewa Faransa ta lashe wasa daya ne kawai daga cikin bakwan data buga a baya a gasar cin kofin duniya.

Har ila yau kwallaye uku kacal Faransar ta zira a wadancan wasanni bakwai.

A yanzu dai Uruguay ce kan gaba a wannan rukuni na A da maki hudu, bayan da ta doke Afrika ta Kudu da ci 3-0 a jiya.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.