Girka 2-1Najeriya

Karawa tsakanin Najeriya da Girka
Image caption A yanzu zai yi wuya Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na gaba

Kasar Girka ta doke Najeriya da ci 2-1 a karawar da suka yi a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

A minti na 16 ne dan wasan Najeriya Uche ya fara zura kwallo bayan wani firi kik da aka buga.

Sai dai 'yan wasan Najeriyar sun fara gazawa bayan da alkalin wasa ya kori Sani Kaita, bayan da ya taka dan wasan Girka da gangan.

Abinda ya baiwa Girkan damar mamaye wasan, inda ta kuma rama kwallon ta mintuna biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo Girka ta ci gaba da kai hare-hare, amma sai a minti na 72, sannan suka samu kan su inda suka zira kwallo ta biyu.

To a yanzu haka dai tuni masana wasan kwallon kafa sun fara tsokaci a kan yadda yan wasan Nigeria suka taka wannan kwallo.

Yanzu haka dai yayin da wasu da dama ke dora alhakin rashin nasarar ta Nigeria a kan Sani Kaita, wasu kuwa na ganin matsalar na ga dukkanin 'yan wasan na Nigeria.

Masu wannan ra'ayi na ganin cewar yan wasan na Najeriya ba su taka rawar gani a wasan ba.

A hali yanzu kuma Shi Sani Kaita ya nemi gafarar daukacin Yan Najeriya game da hallayar da ya nuna wadda ta janyo masa kora.

Yanzu dai sai a wasan karshe ne za a san makomar Najeriya, ganin cewa Argentina wacce ta lashe wasanni biyu, ta tsallake zuwa zagaye na biyu.