An sabunta: 18 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:04 GMT

Karawa tsakanin Ingila da Aljeriya

Karawa tsakanin Ingila da Aljeriya

Wasu masu sha'awar kwallon kafa suna shirin shiga kallon wasan

Bayan da maki biyu ya kufce mata a wasan farko, Ingila na bukar ganin ta farfado a karawar da za ta yi da Aljeriya a garin Cape Town a rukunin C.

Kuma sun samu kwarin guiwa da dawowar Gareth Barry, wanda ya samu rauni ana gab da za a fara gasar.

A daya bangaren Aljeriya na fatan ganin ta yi kokari a wannan karon, bayan da ta sha kashi a hannun Slovaniya a wasan farko.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Sai dai za su yi wasan ne ba tare da Abdelkader Ghezzal ba, bayan da ya samu jan kati a wasan da ya gabata.

Daga cikin 'yan wasan da ake saran za su taka rawar gani sun hada da Wayen Roony, wanda ya bayyana cewa yana saran zira kwallo a wasan na Aljeriya. Baya ga Roony, a kwai Rafik Saifi a bangaren Aljeriya.

Har ila yau a kwai Steven Gerrard da Karim Ziani, wadanda duk suna taka rawa sosai a kasashen na su.

Wannan wasa dai nada mahimmanci domin shi zai nuna alkiblar kasashen biyu a wannan rukuni.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.