An sabunta: 18 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 13:45 GMT

Sabiya 1 Jamus 0

Karawa tsakanin Jamus da Serbia

A wasan farko Jamus ta lallasa Australiya da ci 4-0

A karawar da aka yi da Jamus da Sabiya, kasar Jamus ta kwashi kashinta a hannu, inda aka tashi Sabiya na da ci daya, Jamus na nema.

An kuma kori dan wasan kasar Jamus daya a wasan.

Jamus ta yi fatan ganin ta dora akan nasarar da ta samu a kan Australiya, sai dai hakan bai samu ba.

Nasarar da kasar Sabiya ta samu, ya sanya a yanzu komai na iya kasancewa a rukunin D na gasar ta cin kofin duniya.

A yanzu dai Sabiyan ta bi sahun kasashen Jamus da Ghana wajen samun maki uku-uku, hakan na nufin kowacce za ta dage don ganin ta samu nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.