Brazil ta lallasa Ivory Coast.

Brazil ta lallasa Ivory Coast
Image caption Brazil ta lallasa Ivory Coast

Brazil ta lallasa kasar Ivory Coast da ci uku da guda a gasar cin kofin duniya a wasa na biyu da kasashen suka buga a rukunin G.

Dan wasan Brazil Fabiano ne ya zura kwallon farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan bayan da aka dawo hutun dan wasan ya zura ta biyu.

Kafin dai dan wasan ya zura kwallon ya taba da hannu har sau biyu amma alkalin wasa ya bada kwallon.

Elano ne ya zurawa Brazil kwallon ta ta uku a cikin minti sittin da uku.

Drogba ya samu fanshewa Ivory Coast kwallo guda ne a minti saba'in da tara na wasan.

Kafin a kammala wasan dai an nunawa Kaka jan kanti cikin minti tamanin da takwas.

Brazil yanzu dai ta tsallake zuwa zagaye na biyu a yayinda take da maki shida.

A wasan farko da Brazil din ta buga da Koriya ta Arewa, an tashi wasan ne da ci daya da guda, inda Brazil ta yi nasara.