Slovakia 0 Paraguay 2

Slovakia 0 Paraguay 2
Image caption Slovakia dai bata taka rawar gani a wasan ba.

Paraguay ta doke Slovakia da ci biyu da nema a wasa na biyu da kasashen biyu suka buga a rukunin F.

Dan wasan Paraguay Enrique Vera ne ya zura kwallon farko ana minti ashirin da shida da fara wasan.

Sanan kuma ana sauran minti biyar a kammala wasan Riveros ya zura ta biyu.

Yanzu haka dai Paraguay na da maki hudu ne a rukunin yayinda Slovakia take da maki guda.

A wasan farko da Paraguay ta buga da Italiya a rukunin, an tashi wasan ne daya da yada.