Ana barazana ga rayuwar Sani Kaita

Sani Kaita
Bayanan hoto,

Sani Kaita, lokacin da alkalin wasa yake korar sa

Dan wasan Najeriya Sani Kaita ya samu fiye da sakonni 1,000 da ke barazana ga rayuwar sa, bayan da ya samu jan kati a wasan Najeriya da Girka, a gasar cin kofin duniya.

"kaita ya samu sakonni fiye da 1,000 ta hanyar e-mail daga Najeriya," a cewar mai magana da yawun tawagar kasar Peterside Idah.

"Muna daukar wannan lamarin da mahimmanci sosai. Mun yi magana da gwamnatin Najeriya, kuma mun rubutawa hukumar kwallon kafa ta Fifa."

Najeriya na kan gaba da ci 1-0, lokacin da Kaita ya taka dan wasan Girka Vassillis Torosidis a minti na 33.

Daga bisani Girkan ta lashe Najeriya da ci 2-1, abinda ya jefa makomar kasar a wannan gasa cikin rudani.

"Muna daukar abinda mahimmanci, saboda wannan wani matashi ne da ke yiwa kasar sa hidima dama kwallon kafa," in ji Idah.

Idah ya kara da cewa hankalin Kaita, dan shekaru 24 ya tashi, amma yana samun goyon baya daga sauran 'yan wasan da kuma shugabannin su".

Najeriya za ta kara da Koriya ta Kudu a ranar Talata, kuma tana bukatar yin nasara domin samun duk wata dama ta tsallakewa zuwa zagaye na biyu.