An sabunta: 21 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 09:16 GMT

Karawa tsakanin Portugal da Koriya ta Arewa

Karawa tsakanin Portugal da Koriya ta Arewa

Portugal ta tashi babu ci a wasan ta na farko na Ivory Cost

Bayan ta tashi babu ci tsakanin ta da Ivory Cost, Portugal na bukatar lashe wannan wasan domin karfafa damar ta ta tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Haka kuma Cristiano Ronaldo, zai yi fatan ganin ya cimma fatan da magoya bayan kasar da sauran jama'a keda shi a kansa, ta hanyar taka rawar gani sosai.

Sai dai duka shi da sauran 'yan wasan Portugal na hasashen fuskantar tirjiya daga Koriya ta Arewa, musamman ganin yadda ta kaya tsakanin ta da Brazil.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci dai sannan Brazil ta samu kanta a wancan wasa.

Daga cikin 'yan wasan da za su iya jan hankalin jama'a a wasan sun hada da Ricardo Carvalho da Jong Tae Se, kuma za su fafata ne gaba-da-gaba.

Baya ga su kuma ana saran dan wasan da yafi kowanne tsada a duniya, Ronaldo, zai taka rawar gani a wannan wasa, amma zai fuskanci matsi daga 'yan wasan Koriya.

Portuganl ce dai ta lashe karawar da kasashen biyu suka yi a gasar 1966, da ci 5-3, amma bayan Koriya ta fara zira mata kwallaye 3.

"Dole ne muyi wasa da zafi domin muna bukatar nasara ruwa a jallo," in ji kociyan Portugal Carlos Queiroz.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.