Portugal 7-0 Koriya ta Arewa

Karawa tsakanin Portugal da Koriya ta Arewa
Image caption Karawa tsakanin Portugal da Koriya ta Arewa

Portugal ta lallasa Koriya ta Arewa da ci bakwai da nema a wasan da suka buga a rukunin F, a ci gaba da gasar cin kofin duniya.

Raul Meireles ne ya zira kwallon farko a minti na 19, kafin Tiago ya zira kwallaye biyu, sannan Simao da Almeida da kuma Ronaldo da Liedson suka zira kwallaye dai dai.

Koriya ta Arewa ta ci gaba da kokartawa har aka tafi hutun rabin lokaci, amma bayan an dawo sai labari ya kara shan ban ban, inda cikin minti bakwai Portugal ta zira kwallaye uku.

Simao ne ya zira kwallo ta biyu a minti na 53, yayinda Almeida ya zira ta uku a minti na 56, kafin Tiago ya ci ta hudu a minti na 60.

Yayinda a minti na 81, Liedson ya zira kwallon ta biyar jim kadan bayan shigowar sa wasan daga benchi.

Ronaldo ya kara ta shida a minti na 87, sannan Tiago ya zira kwallon shi ta biyu a minti na 89.

Har yanzu dai Portugal bata tsallake zuwa zagaye na biyu ba, sai an buga wasa na gaba a rukunin tukunna, inda za ta kara da Brazil, sannan Ivory Cost ta kara da Koriya ta Arewa.