An sabunta: 22 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 11:02 GMT

Karawar karshe a rukunin A

A yau ne ake yin ta ta kare a rukunin A a gasar cin kofin duniya da ake ci gaba da fafatawa a Afrika ta Kudu.

Mai masaukin baki Afrika ta Kudu za ta kara da Faransa, wasan da kowannen su ke bukatar lashewa domin samun damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

Duka Faransa da Afrika ta Kudu suna da maki dai dai ne, kuma za su samu kansu ne kawai tala'akari da yadda za ta kaya a daya wasan.

Baya ga wannan a yau ne kuma za a fara sanin makomar kasashen Afrika a gasar ta bana.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Wasan na biyu

A daya bangaren za a fafata ne tsakanin Mexico da Uruguay, dukkanin su nada maki hurhudu, kuma idan suka ta shi babu ci, to dukkan su za su tsallake zuwa zagaye na gaba.

Duka Mexico da Uruguay na fatan ganin sun tsallake zuwa zagaye na gaba, abinda yasa ake ganin wasan zai kayatar sosai.

Kasashen biyu sun ja hankalin jama'a ne bayan da suka lashe Afrika ta Kudu da Faransa cikin sauki awasannin da aka buga a baya.

Za dai a buga wasannin ne lokaci guda, kuma ana ganin wasannin na da matukar tasiri ga gasar, musamman idan aka fitar da Afrika ta Kudu saboda kasancewar ta mai masaukin baki.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.