Ingila da Amurka sun tsallake zuwa zagaye na biyu

Magoya bayan Aljeriya
Image caption Magoya bayan Aljeriya jim kadan kafin Amurka ta doke su

Ingila da Amurka sun tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

Ingila dai ta doke Slovaniya da ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi, yayinda Amurka ma ta doke Aljeriya da ci daya.

Hakan na nufin an fatar da Ajeriya da Slovaniya daga gasar ta bana.

Jermain Defoe ne ya zira kwallon a minti na 22 da fara wasa, sannan sukai ta kai hare-hare amma ba tare da nasara ba.

Ana ta bangaren Amurka bata samu kanta ba sai a mintin karshe na wasan, inda London Donovan ya zira kwallo dayan.

A yanzu dai Aljeriya ta zamo kasa ta baya bayan nan daga nahiyar Afrika da aka fitar a gasar. Bayan da a jiya aka fitar da Afrika ta Kudu da Najeriya.