Jamus da Ghana sun tsallake zuwa zagaye na biyu

Jamus da Ghana sun tsallake zuwa zagaye na biyu
Image caption Jamus ce ta jagoranci rukunin D

Ghana ta zama kasar Afrika ta farko da ta tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya dake gudana a kasar Afrika ta kudu.

Jamus dai ce ta jogoranci rukunin D bayan ta doke Ghanan da ci daya mai ban haushi.

Austrailiya kuwa ta yi nasara ne a kan Serbia da ci biyu da daya, amma duk kasashen biyu sun fita daga gasar.

Jamus ta kare ne da maki shida a rukunin a yayinda Ghana wanda ta zamo na biyu ta kare da maki hudu. Ita ma dai Austrailiya ta kare da maki hudu amma dai an zura mata kwallaye da yawa.