An sabunta: 25 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 11:10 GMT

Karawar karshe a rukunin G

Duka Brazil da Portugal za su shiga wasan ne bayan kyakkyawar rawar da suka taka a wasannin su na baya.

Ita dai Brazil ta doke Ivory Cost ne da ci uku da daya, yayinda Portugal da lallasa Koriya ta Arewa da ci bakwai da nema.

Tuni dai Brazil ta riga ta tsallake zuwa zagaye na biyu, yayinda Portugal da Ivory Cost ke neman cike gurbin da ya raeg a rukunin na G.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Ita dai Ivory Cost za ta kara ne da Koriya ta Arewa wacce tuni aka fitar da ita daga gasar, kuma tana bukatar ta doke ta da akalla kwallaye tara, sannan tayi fatan Brazil ta lashe Portugal.

Idan ba haka ba kuwa to Portugal ce za ta bi sahun Brazil a wannan rukuni.

Wani abu da ke kara karfafawa Portugal guiwa shi ne na ganin cewa koda an tashi canjaras to itace za ta kai labari.

Ivory Cost dai na neman zamowa kasa ta biyu daga nahiyar Afrika data tsallake zuwa zagaye na biyu, bayan da Ghana ta zamo daya tilo da ta yi hakan.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.