An sabunta: 25 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:44 GMT

Karawar karshe a rukunin H

Wannan shi ne karo na baya bayan nan da Spaniya za ta kara da Chile, kuma za a iya cewa wannan itace za ta zamo mafi mahimmanci ga kasar ta Spaniya.

A yanzu dai Chile ce ke kan gaba a wannan rukuni na H, da maki shida, yayinda Spaniya da Switzerland keda maki uku uku, kuma tana bukatar a tashi babu ci domin ta tsallake zuwa zagaye na biyu.

Har ila yau Chile ka iya tsallakewa koda Spaniya ta doke ta, muddum dai Switzerland ba lashe Honduras da kwakwalai masu yawa ba.

Hankalin jama'a dai zai fi karkata ne kan yadda za ta kaya tsakanin Spaniya da Chile, ganin Spaniyan na daga cikin kasashen da ake zaton za su lashe gasar.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Amma sai ta fara gasar da kafar baya, bayan da Switzerland ta lashe ta a karawar farko.

Ita dai Switzerland za ta kara ne da Honduras, kuma tana bukatar samun nasara domin kaiwa ga gaci.

Sai dai Switzerland na da kwarin guiwar lashe wannan wasa ganin cewa Honduras bata lashe wasa ko daya ba kawo yanzu.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.