Uruguay ta doke Koriya ta Kudu

Suarez ne zira kwallaye biyu a wasan
Image caption Suarez ne zira kwallaye biyu a wasan, kuma suna jiran Ghana ko Amurka

Uruguay ta doke Koriya ta Kudu da ci biyu da daya a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu.

Hakan dai ya bata damar tsallakewa zuwa zagayen kusa da na kusa da karshe, inda za ta kara da kasar da ta samu nasara tsakanin Amurka da Ghana.

Uruguay ce ta fara zira kwallo na farko tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ta hannun Suarez.

Amma bayan an dawo sai Koriya ta bude wuta tana kai munanen hare-hare, inda daga bisani ta rama kwallen ta.

Haka dai aka ci gaba da kai ruwa rana, har zuwa minti na 79, inda Suarez ya kara zira kwallon sa ta biyu, abinda kuma ya baiwa Uruguay damar lashe wasan.