An sabunta: 27 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 13:09 GMT

Karawa tsakanin Jamus da Ingila

Wasan da Jamus da Ingila za su buga shine karo na biyar da kasashen biyu za su taka leda a gasar cin kofin duniya.

A wasan da suka buga a gasar da aka shirya 1966, Ingila ce ta yi nasara sai kuma Jamus ta yi nasara a shekarar 1970, kuma suka buga kunnen doki a shekarar 1982 da 1990.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

A tarihi dai kasashen biyu sun buga wasanni ashirin da bakwai tsakaninsu inda Ingila ta lashe wasa 12, Jamus kuma ta lashe goma.

Ingila da Jamus sune kawai ke da 'yan wasa ashirin da uku gabaki daya da ke taka leda a kungiyoyin kasar su.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.