An sabunta: 28 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 15:44 GMT

Karawa tsakanin Brazil da Chile

Dan wasan Brazil Kaka zai taka leda bayan dakatarwa da aka yi mai sakamakon jan katin da aka nuna mai a wasan da kasar ta buga da Ivory Coast, yayinda kuma Elano ya murmure bayan raunin da ya samu a sahur kafarsa a wasan.

Chile dai ba za ta samu amfani da 'yan wasanta uku ba, saboda an dakatarda su.

Shi dai Marco Estrada an sallame shine a wasan a kasar ta buga da Spain, sai kuma an nuna wa Waldo Ponce da Gary Medel katin gargadi guda biyu a wasanni biyu a gasar.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Duk kasashe biyar dai da suke wakilcin kudancin Amurka sun kai zuwa zagaye na biyu amma ga dukkan alamu za a fidda daya daga cikin su.

A wasan share fage da Brazil din ta buga da Chile, Brazil ta lallasa Chile a wasan da aka buga aiago da ci uku da nema a yayinda kuma a wasan na biyu aka tashi hudu da biyu, Brazil din ta sake nasara.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.