Capello zai tattauna da jami'an FA

Fabio Capello
Image caption Fabio Capello bai ji dadin wannan gasar ba kwata-kwata

Kociyan Ingila Fabio Capello ya ce ba zai ajiye mukamin sa ba, amma zai tattauna da jami'an hukumar kwallon kafa ta Ingila wato FA, bayan da aka fitar da kasar a gasar cin kofin duniya.

Jamus ce ta fitar da Ingila a zagaye na biyu a gasar, bayan da ta lallasata da ci 4-1.

"Ina da lokaci domin yanke shawara, amma sai na tattauna da shugaban FA Sir Dave Richards tukunna," in ji Capello dan shekaru 64.

Da aka tambaye shi ko zai yi murabus, sai yace: "Sam sam ba zan yi ba. Mu jira tukunna sai na koma London."

Ana saran zai yi karin bayani kan matsayin sa a wani taron maneman labarai da za su gudanar.

Gab da za a fara gasar ne dai ya kara sanya hannu kan wata kwantiragin da ta bashi damar kasancewa a Ingila har zuwa shekara ta 2012.

Game da wasan da aka buga, Capello yace kin amincewa da kwallon da Lampard yaci shi ne abinda ya tantance makomar wasan.