FIFA ta nemi afuwa daga Ingila da Mexico

FIFA ta nemi afuwa daga Ingila da Mexico
Image caption Lokacin da alkalin wasa ya hana kwallon da Lampard ya zura.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter, ya nemi afuwa daga hukumar FA ta Ingila, bayan da alkalin wasa ya hana kwallon da Lampard ya ci a wasan Ingila da Jamus.

Blatter ya ce kuskuren ya sa shi sake tunani domin sake tattaunawa kan amfani da na'urar zamani a taron hukumar FIFA na watan gobe.

An soke kwallon da Lampard ya zira a wasan da Jamus ta doke su da ci 4-1, duk da cewa kwallon ta haura layi.

Har ila yau Mista Blatter ya nemi afuwar Mexico bayan da ta tabbata cewa Carlos Tevez ya yi satar gola a wasan da suka buga da Argentina. Ana ganin da an bada kwallon ta Lampard da ta sauya yanayin wasan.

Irin wannan kuskure ya janyo kiraye-kirayen amfani da fasahar zamani domin taimakawa alkalan wasa, musamman daga kungiyar 'yan wasa ta duniya.