Goodluck ya dakatar da Super Eagles

Tawagar Super Eagles ba ta lashe wasa ko daya ba a gasar
Image caption Tawagar Super Eagles ba ta lashe wasa ko daya ba a gasar

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bada sanarwar dakatar da tawagar Super Eagles daga halartar wata gasa na tsawon shekaru biyu, saboda rawar da suka taka a gasar cin kofin duniya.

Mai baiwa shugaban kasan shawara kan harkar labarai Ima Niboro ya shaidawa manema labarai cewar shugaban kasar ya dauki wanan matakin ne domin gyara harkar kwallon kafa a kasar.

Ya ce: "Matakin ya zama dolene ne ganin yadda 'yan wasan kasar suka kasa tabuka komai a gasar cin kofin duniya".

Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi, wanda ya jagoranci kwamitin gwamnatin tarayya na musamman da ya sa ido kan shirye-shiryen kasar a gasar da ta gabata, yace Najeriya za ta aikawa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA domin bayyana mata matakin da ta dauka.

"Mun je gasar cin kofin duniya, kuma mun gano matsaloli da dama a cikin kungiyar don haka muna bukatar komawa domin sake shawara," in ji Amaechi.

Har ila yau shugaba Jonathan ya umarci a gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudaden da aka warewa kungiyar ta Super Eagles a lokacin gasar.

Najeriya ce ta zo ta karshe a rukunin B a gasar ta bana inda ta samu maki daya kacal, abinda yasa 'yan kasar da dama suka nuna rashin gamsuwa da rawar da 'yan wasan suka taka.

Har wa yau dai dokoki Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya wato Fifa ta hana gwamnatoci tsoma bakin cikin al'amuran kwallon kafa a kasashen su.