Del Bosque na fatan kafa tarihi

David Villa
Image caption Kawo yanzu David Villa ya zira kwallaye hudu a gasar ta bana

Kociyan Spaniya Vicente Del Bosque, ya bayyana kwarin guiwar sa game da 'yan kwallon kasar bayan da suka doke Portugal da ci daya mai bai haushi a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya.

Wasan shi ne karo na farko da Spaniya, wacce na daya daga cikin wadanda ake saran za su lashe gasar ta nuna kwarewa sosai, bayan da ta hadu da kwararrun 'yan baya.

"Muna kara samun kwarin guiwa, don haka muna fatan kafa tarihi," a cewar Del Bosque. "Mun sani cewa muna kokari sosai".

Duk da irin nasarar da ta saba samu afagen wasan klub klub, Spaniya ba ta taba lashe gasar cin kofin duniya ba.

Spaniya za ta kara da Jamus ko Argentina - wadanda suka lashe kofin sau biyar a tsakanin su, a wasan kuda dana karshe - idan har ta doke Paraguay a wasan dab dana kusa da karshe ranar Asabar.

Spaniya dai ta sha wuya a hannun Portugal a zagayen farko na wasan, kafin daga bisani kociya Del Bosque yayi amfani da basirar sa, inda ya sauya Fernando Torres da Fernando Llorente.

Kuma daga nan ne suka samo kan 'yan Portugal din, har kuma suka zira kwallo ta hannun David Villa, bayan wani tabe-tabe tsakanin 'yan bayan Portugal din, wanda ya kara nuna kwarewar 'yan wasan na Spaniya.

Haka kuma suka ci gaba da mamaye wasan tare da taka rawar ganin da basu taba yin irin ta ba tun da aka fara gasar ta bana.