An sabunta: 2 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 15:17 GMT

Karawa tsakanin Uruguay da Ghana

Karawa tsakanin Uruguay da Ghana

Wannan ne karo na farko da Uruguay da Ghana ke karawa a wannan mataki

Ghana da Uruguay ba su taba karawa a tsakanin su a gasar kasa da kasa, kuma za su kara ne a filin wasa na Soccer City, a zagayen gab dana kusa da karshe.

Ita dai Ghana na fatan kafa tarihi ne domin zamowa kasa ta farko da ta kai zagayen kusa dana karshe daga nahiyar Afrika.

Kuma za ta dogara ne kan 'yan wasan ta irin su Asamoah Gyan da John Mensah da kuma Stephen Appiah da Sulley Mutari.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Anata bangaren Uruguay tana kokarin farfado da kimarta ne afagen kwallon kafa, bayan da ta shafe shekaru ba ta yin wani abu na azo a gani.

Duk da cewa kasar ta taba lashe gasar cin kofin duniya a baya, amma yau shekaru talatin kenan rabon ta data kawo wannan matakin.

Kuma za ta dogare ne kan 'yan wasan ta irin su Suarez da Diego Forland domin su fitar da ita kunya.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.