Spain 1-0 Paraguay

Karawa tsakanin Spain da Paraguay
Image caption Karawa tsakanin Spain da Paraguay

Kasar Spain ta yi nasarar shiga zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya bayan da tai nasara kan Paraguay da ci daya da nema.

Dukkan kasashen sun taka rawa sosai a wasan, inda suka sami bugun daga kai sai mai tsaron gida amma suka zubar.

Yanzu haka dai kasar ta Spain ta bi sahun Holland da Jamus da Uruguay a matsayin kasashen da za su yi karawar kusa da ta karshe.

Tun farko dai Jamus ta lallasa Argentina da ci hudu ba kowa daya a zagayen dab da na kusa da na karshen.

Za a kara ne a wasannin kusa da na karshe tsakanin Holland da Uruguay, ita kuma Jamus ta kara da Spain.