Maradona na tunanin ajiye aikin shi

Maradona na tunanin ajiye aikin shi

Kocin Argentina Diego Maradona ya ce yana duba yiwuwar ajiye aikinshi a matsayin kocin kasar bayan Jamsu ta lallasa 'yan wasan sa a gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa.

"Zan iya bari gobe," Inji shi bayan Jamus ta doke Argentina da ci hudu da nema.

"Ina son inyi tunani mai zurfi sanan kuma inyi shawara da iyalai ne kafin in dauki wani mataki".

Maradona, ya jagoranci tawagar Argentina a matsayin dan wasa a gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 1986 inda Argentina ta dau kofin.