Akwai shakku a kan Fabregas

Cesc Fabregas
Image caption Cesc Fabregas

Akwai shakkun cewar dan wasan Spaniya Cesc Fabregas ba zai taka leda ba a wasan kusa da na karshe da kasar za ta buga Jamus a ranar Laraba saboda ya samu raunin a lokacin da yake horo.

Fabregas dai ya dingisa ya bar filin wasa ne a Potchefstroom a ranar litinin.

An dai gwada dan wasan a kafarsa inda ya samu rauni, kuma likitoci sun tabbatarda cewar bai karye ba.

A watan Maris din ya gabata ma dan wasan mai shekarun 23 ya samu rauni a kafarsa amma ya warke kafin a fara gasar cin kofin duniya.

Barcelona dai na neman siyan dan wasan wanda ke takawa kungiyar Arsenal leda.