An sabunta: 6 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 10:46 GMT

Karawa tsakanin Uruguay da Holand

Karawa tsakanin Uruguay da Holand

Holand ta doke Brazil da ci 2-1 a wasan dab dana kusa dana karshe

A dai dai loakcin da ake komawa fagen fama a zagayen kusa dana karshe na gasar cin kofin duniya, inda Uruguay za ta kece raini da Holand a birnin Cape Town.

Magoya bayan kasashen biyu na ci gaba da hallara a birnin na Cape Town, domin kekeshe kwarkwatar idanun su.

A na dai yiwa Uruguay kallon kasar da ta yi bazata a gasar ta bana, ganin cewa itace ake ma kallon mafi rauni a cikin kasashen da suka fito daga Kudancin Amurka.

Yayinda akewa Holand kallon daya daga cikin kasashe mafi karfi a gasar, musamman bayan da ta doke Brazil a wasan dab dana kusa na karshe.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Tuni dai kociyan Uruguay Oscar Tabarez, yace za su yi iya kokarin su domin hana dan wasan Holand Ian Robben damar kaiwa-da-komowa a wasan.

Yayinda ana shi a bangern kociyan Holand Van Marwijk, yace dole ne yaran sa su maida hankali ganin irin rawar da Uruguay ta taka a baya.

Uruguay za ta buga wasan ne ba tare 'yan wasanta uku ba ciki har da Suarez, wanda ya samu jan kati a wasan su da Ghana, yayinda Holand za ta yi ba tare da 'yan wasa biyu ba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.